Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola yace ƙasar nan bazata cigaba da dogaro da wasu ƙasashe domin samun magani a lokacin ɓarkewar cutar Covid-19.
Fashola wanda shine shugaban gidauniyar Nazarin Harkokin Lafiya ya bayyana haka a taron daya wakana a kafar sadarwa ta yanar gizo, wadda gidauniyar ta shirya a ranar Talata a Lagos.
Yayi nuni dacewar
akwai buƙatar ƙarfafa wa mutane gwuiwa wajen yin bincike a ɓangaren lafiya, domin gano hanyoyin da za’a samar da magunguna a cututtukan dake damun mu, da sauran cututtuka kamar Covid-19.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugabannin Kungiyar G20 Sun Amince Zasu Kara Azama Kan Ayyukan Jin Kai A Kasar Afghanistan
Tsohon Gwamnan yace an ƙirƙiri gidauniyar domin samun kuɗaɗe tare da bunƙasa harkokin bincike a ɓangaren lafiya da zasu amfani ƴan Najeriya.
Fashola yace “bazamu cigaba da dogaro da wasu ƙasashen duniya domin samun rigakafi a wannan lokacin ba.
A cewar sa, gidauniyar na son samun biliyan 10 domin fara aiwatar da bincike a ɓangaren lafiya.
A jawabin sa, Sarkin Kano na 14 Lamiɗo Sanusi kuma mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar yace lokaci ne da ƙasar dazata gane kanta, tare da inganta samun ilmi da lafiya