Ba zamu daina Yajin Aiki ba — ASUU
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a ranar Litinin ta ce ta jajirce wajen samun haɗin kan da ake buƙata ga Jami’o’in gwamnati.
Kungiyar ta ce ba za ta sadaukar da jin dadin mambobinta ba, kuma za ta bijirewa duk wani yunƙuri na mayar da masu ilmi a matsayin bayi, kan shugabanci marar kyau
Shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, wanda ya bayyana haka a Ibadan, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da ikirarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na cewa ta biya buƙatun Ƙungiyar sai dai ta hana su Albashi.
“Mun jira tsawon watanni 14 daga Disamba 2020 zuwa Fabrairu 2022 kafin mu ayyana wannan yajin aikin. Ina cewa sanarwar watanni 14, watanni 14 na alkawari, kuma Hukumar Kula da Addini ta Najeriya (NIREC) ta shiga tsakani a shekarar 2021 lokacin da za mu ayyana yajin aikin. Mun ba su wata daya babu sakamako. Jarumai sukan mutu kafin a yaba su, amma kungiyar mu ba za ta mutu ba. Ba za mu mutu ba. Za mu kasance a raye don ganin an shawo kan wannan gwagwarmaya,” in ji shi.
Akinwole ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta saka Naira Tiriliyan 1.1 a Asusun farfaɗo da jami’o’in gwamnati ta hanyar na NEEDS, a rahoton tantance wa kan yadda Jami’o’in Gwamnatin Najeriya suka lalace.
A wani labarin kuma: B/Haram Sun Shiga wani hali suna fama da Ƙarancin Abinci, Makamai, bayan Ambaliyar Ruwa
Daruruwan ‘yan Boko Haram da iyalansu ne suka bar sansanoninsu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi barna a matsugunan su, lamarin da ya tilasta musu yin kaura zuwa wasu wurare da ke gefen dajin Sambisa, kamar yadda Daily Trust ta gano.
Daily Trust a baya ta ruwaito yadda mayaka 70 suka nutse tare da kashe maharan sama da 200 da suka hada da kwamandoji biyar biyo bayan harin da sojojin Najeriya suka kai a karshen mako. An tattaro cewa ambaliya da kogin Yedzaram ya yi ya shafi sansanonin ‘yan ta’adda da dama a Sheuri, da Mazaɓar Kumshe da Gaizuwa a ranar Lahadi da safe kuma ya sa aka koma wurin.