By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren ta’addancin da aka kai a kananan hukumomin Kanam da Wase na jihar Filato, inda ya bayyana kashe-kashen a matsayin munana.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Talata a Abuja, shugaban ya ce bai kamata a bar wadanda suka aikata laifin su tsira daga shari’a ba.
DUBA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa Mataimakin Gwamnan Kano Yayi Murabus Daga Mukamin Kwamishinan Noma Da Albarkatun Kasa
“Kada su tsira ko a gafarta musu,” in ji shi.
Ya kuma umarci jami’an tsaro da su yi aiki tukuru da gwamnatin jihar, domin shawo kan lamarin tare da daukar matakin gurfanar da masu laifin cikin gaggawa.
Buhari ya jajanta wa wadanda lamarin ta’addancin ya shafa, inda ya ce a wani lamari mai muhimmanci, dole ne zaman lafiya ya dawo ko ta halin kaka ga jihar da ma kasa baki daya.
“Ina kira ga daukacin al’ummarmu, musamman al’ummar Jihar Filato, da su tona asirin masu aikata irin wannan aika-aika, masu daukar nauyinsu, da masu karfafa irin wadannan miyagun ayyuka da suke aiwatar da wadannan munanan ayyuka na kisan kai, domin doka ta dauki matakin da ya dace.
“Bai kamata a gafarta musu ba,” in ji shugaban. (NAN)