Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada aniyar gwamnatin sa ta ganin an kara samun zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai a fadin jihar nan.
Gwaḿnan ya sanar da hakan yayin rantsar da ‘yan kwamitin wakilan addinai wanda ya gudana dakin taro na Africa House dake fadar gwaḿnatin Kano.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ganduje yace gwamnati ba zata amince wasu tsirarun mutane ciki har da ‘yan siyasa suyi amfani da banbancin addinai wajen haifar da rashin fahimta ba, a tsakanin mazauna jihar.
KARANTA ANAN: Peter Obi ya bayyana abinda suka tattauna da Obasanjo
Ya kara da yin kira ga al’umma da su guji yin amfani da banbancin addini da akida ko kabila a matsayin makamin yakar abokan zaman su.
Gwamnan ya kuma kara da cewa makasudin samar da wannan kwamiti shine don a kara samar da dankon zumunci tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi a jihar Kano domin samun cikakken zaman lafiya da karuwar arziki.
A nasa jawabin Sheikh Bin Usman wanda shine shugaban kwamitin yayi kira ga jagororin addinan biyu da su himmatu wajen fadakar da mabiya mahimmácin dake tattare da zaman lafiya kamar yadda shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen Abuja Bishop Peter Muyiwa ya bayyana mahimmacin hadin kan mabiya mabanbantan addinai wajen dorewar zaman lafiya a jihar kano da ma kasa baki daya.
A wani labarin kuma: Yanzu-Yanzu: Karo Na Bakwai, An Dauke Wutar Lantarki Duk Fadin Najeriya
Wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya tun daga tushe a ranar Litinin, lamarin da ya jefa ilahirin kasar nan cikin duhu. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Lamarin na zuwa ne watanni bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta kaddamar da wani shiri na musamman domin wadatuwar wutar lanatarki a fadin Najeriya.