Daga: Abbas Yakubu Yaura
Zababben Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, a jiya Lahadi yace, gwamnatinsa ba za ta binciki Gwamna Adegboyega Oyetola ba idan aka rantsar da shi a matsayin Gwamna.
Ya ce duk da cewa kwamitin mika mulki ba ya samun cikakken hadin kai daga gwamnati mai ci, yana sa ran lamarin zai sauya kafin ranar mika mulki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nishadi: Don Kana Kashe Kudade A Kaina Baka Da Tabbacin Samun Soyayyata – Jaruma Sandra Ifudu
Kakakin zababben gwamnan, Olawale Rasheed ya ce gwamnatin mai jiran gado na da niyyar bayyana manufofinta cikin gaggawa bayan ta yi nazari kan takardar mika mulki da gwamnatin mai barin gado za ta shirya, inda ya ce babu wata hanyar cin amana tsakanin gwamnati mai ci da mai barin gado.
Mista Rasheed ya ce: “Babu wani nau’in cin amana a tsakaninmu. Ya zama al’ada irin wannan tashe-tashen hankula na faruwa idan aka samu sauyin gwamnati tsakanin bangarorin biyu. Muna fatan za mu sami karin hadin kai yayin da muke ci gaba.
“Ba za mu binciki gwamnatin yanzu ba. Abin da za mu yi shi ne kawai mu shiga cikin bayanan mika mulki don sanya al’amura a hankali kafin bayyana sanarwar manufofinmu.
“Bincike mulki kuma zai kai ɓata lokaci mai daraja na sabuwar gwamnati da kuma tsammanin mutane daga gare mu; hakan zai yi mana tsada.
“Ya zuwa yanzu dai, mun kafa kwamitin rikon kwarya da zai yi hulda da gwamnati domin a samu saukin sauyin yanayi, duk da cewa ba mu samu yadda muke zato ba.”
“Mun mika musu wasikar kuma an amince da ita, don haka muna sa ran samun cikakken hadin kai.”