Gwarzuwar yar wasan Tennis na Duniya kuma wacce ta lashe zinare karo hudu a gasar Olympic Serena Williams ta ce ba za ta shiga gasar Olympic da za a fafata a birnin Tokyo na kasar Japan ba muddin ba za a barta ta shiga da jaririyarta ba.
Da ma dai tuni aka yanke shawarar haramta wa yan kallo shiga gasar ta bana don gudun yaduwar annobar Korona.
Kazalika su ma yan wasan ba za a barsu su yi mu’amala da waɗanda ba yan wasa ba, duk dai an yi haka ne don gudun warwatsa cutar mai muguwar illa a kasashen turawa.
Kuma Kasar Japan ta rufe iyakarta inda ta haramta wa kasashe sama da 150 shiga ciki har da kasar Amurka muddin ba a samo wata mafita ta dakile Covid-19 ba.
Gasar ta Olympic za ta gudana ne daga ranar 24 ga watan gobe, makonni biyu kenan bayan gasar Tennis ta mata ta Wembledon, gasar da Williams ta lashe har karo bakwai.
Kazalika za a karkare shi ne a ranar 1 ga watan Agusta, kwanaki 29 gabannin gasar US Open.