Ba zan iya yiwa Tinubu aiki ba bayan sakamakon zaben Ekiti – Segun Oni
Tsohon gwamnan Ekiti, Segun Oni ya musanta yin aiki da Bola Tinubu, ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a karshen mako ta mai magana da yawunsa, Jackson Adebayo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu lokacin mai dawa kura aniyar ta ne, dole Buhari ya yi wa Tinubu kamfen – Onanuga
Oni, dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party, SDP a zaben da ya gabata ya mayar da martani ga kalaman Oyetunde Ojo da kuma Kudu maso Yamma, SWAGA.
Ya karyata ikirarin hadin gwiwa da tsohon Gwamna Ayo Fayose na tabbatar da burin Tinubu na zama Shugaban Ƙasa.
Wanda ya kira shi “kalaman rashin gaskiya kuma karya ce mai arha”, Oni ya bayyana cewa ba zai iya yiwa tsohon gwamnan Legas aiki ba.
Sanarwar ta yi zargin cewa sawun Tinubu “ya bayyana sosai a zaben gwamnan Ekiti da ya gabata na magudin zabe”.
Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC mai mulki ya lashe zaben 18 ga watan Yuni 2022.
Oni ya ce ba kamar Osun ba, ba a ba lauyoyinsa damar duba na’urorin tantance masu kada kuri’a ba (BVAS) duk da umarnin kotun da ta baiwa INEC sau biyu.
Tsohon gwamnan ya ce ya sha fama da rashin nasarar zabe a baya da kuma rashin adalci a kotu wanda mutum daya ya shirya shi a shekarun baya.
Oni ya yi gargadin cewa kada mutane su wuce gona da iri, inda ya kara da cewa shi ba ya cikin harkar gudanar da harkokin siyasa.
A wani labarin kuma: Karancin Naira: Kai Jarumi ne na wannan lokacin – FFK ya yabawa El-Rufai kan caccakar Buhari
Saura mako guda da gudanar da zaben shugaban kasa, mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu, Shettima Bayo Onanuga, ya dage cewa shugaban nasa ya cancanci goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.