Fadar shugaban Najeriya ta musanta rahotannin da ta ce ake yada wa a shafin intanet na neman Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tazarce.
Hakan na kunshe ne a wani sako da kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa shugaban mai kaunar mulkin demokradiyya ne, don haka ba zai taba yunkurin tsawaita mulkinsa ba.
Ya kara da cewa shugaban zai sauka daga mukaminsa bayan kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2023, kuma za a yi sabon zabe ba tare da ya sake tsayawa takara ba.
Malam Garba ya ce “abu ne mai muhimmanci a gane cewa a baya an yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki, domin shugaban wancan lokaci ya yi wa’adi na uku. Hakan ba daidai ba ne kuma ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma gara da aka dakile yunkurin.”
“Babu wani yanayin da zai sa shugaba Buhari ya nemi gyara kundin tsarin mulki don sauya wa’adi biyun da yake da na zama shugaban kasa,” in ji kakakin.
Fadar shugaban kasar ta kuma nisanta shugaban da yunkurin da ta ce wasu na yi na fitowa kan titunan kasar don kira ga shugaba Buhari ya nemi wa’adi na uku.