Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba zai taba sanya baki a aikin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa na EFCC ke yi ba dangane da ayyukanta wajen bankado wadanda ake zargi da rashawa tare da hukunta su.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin bikin yaye jami’an EFCC 328 da ya gudana a NDA dake Kaduna. An gudanar da faretin ne bayan jami’an EFCC din sun kammala horon watanni 13 a fannoni daban-daban domin samun horan akan abin da ya shafi dokoki.
Shugaban kasar wanda Sakataren gwamnati Boss Mustapha ya wakilce shi, ya taya jami’an EFCC din murna kammalawa, inda ya shawarce su akan su dage wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.