Matar Yul Edochie ta farko, May Edochie, ta mayar da martani ga uzurin da mai gidanta ya bata na bukatar karin auren wata matar.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Sai dai matar ta sa ta yi bore ga bukatar tasa duk da uzurin da ya bata na yana da bukatar yin hakan.
KARANTA KUMA Yan San Sun Cafke Wata Mata Bisa Kashe Dan Kishiyarta
Ta ce ba za a tilasta mata ta karbi auren wata matar fiye da daya ba.
Yul, a ranar Laraba, ya raba hoton May, yana rokon ta da ta gafarta masa ya yi karin auren mata ta biyu.
Ya ce ba shi da niyyar maye gurbin watan May din.
Ya yi ikirarin cewa ya nemi gafararta sau da yawa saboda yana neman auren mace fiye da daya.
A Wani Labarin Kuma Kudin Inshorar Motoci Yanzu Ya Karu Zuwa N15,000 Daga N5,000 – NAICOM
Hukumar Inshora ta Kasa (NAICOM) ta kara kudin inshorar masu ababen hawa Sashi na Uku daga Naira 5,000 zuwa Naira 15,000 duk shekara daga Janairu 2023.
Amincewar tana ƙunshe ne a cikin da’ira: NAICOM/DPR/CIR/46/2022 ga kamfanonin inshora da kwanan watan 22, ga watan Disambar 2022.