Sanatan dake wakiltar Kano ta Tsakiya a majalissar Dattijai Sanata Ibrahim Shekarau ya ce, ba zai yi murabus daga siyasa ba har sai ya mutu.
Ya yi wannan ikirarin ne loakcin da yake zantawa da manema labarai bayan rantsar da majalisar Shura ta jihar Kano, inda Shekarau ya ce “Ban da lokacin yin murabus daga siyasa har sai na mutu.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki wani yanki a Kudincin Kaduna
Sanata Ibrahim Shekaru dai ya yi gwamnan jihar Kano har sai biyu , ya Kuma rike mukamin Miinistan ilimi daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
“A takaice, abinda yasa na zo inaw wannan batu shine, in musanta rade-raden da ke cewa, zanyi murabus. A wurina gaskiya babu ranar murabus dina daga siyasa.”
“Kuma kusan shekara 20 kenan Ina fadin irin wannan maganar. Siyasata ita ce addinina, addinina shine siyasata, kuma babu lokacin da zan yi murabus daga addinina sabida dukkannin biyun suna tafiya ne tare” inji shi
“Addini shine bautawa Ubangiji, kuma kololuwar bautawa Ubangiji shine bautawa jama’a, da suka kasance halittar Ubangiji. Kamar yadda na sani Musulunci ya koyar da mu cewa, duk wani taimako da ka bai wa wani, kana cika umarnin Ubangiji ne. Idan na yi maka addu’a ko kyautatawa, nau’in ibada ne”
“A don haka ne yasa nake tausayin duk wanda ya ce zai bar siyasa. Ta yuwu bai fahimci mene ne siyasa ba. Sun tsayar da ita a samun mukami, fita takarar gwamna, sanata ko wani mukami”
“A fahimta ta, siyasa ita ce kwarewar mutum wurin mu’amala da jama’a tare da bautawa jama’a ta duk hanyar da ta kama. Don haka bani da ranar murabus daga siyasa. Ina nan har sai na mutu.