Wani sanatan ƙasar Amurika dan jam’iyar Democract da ya zamo mai adawa da fadar white house ya dauki hankali Al’umma Washington bayan da ya bayar da sanarwar nuna goyon bayan sa hmga daya daga cikin manufofin shugaba Joe Biden.
Joe Manchin yace yanzu ya goyin bayan kudirin nan na ƙara yawan haraji , da yaƙi da sauyin yanayi da kuma rage kuɗaɗen magunguna.
To amma shugaba Biden na Buƙatar goyon bayan dukkanin sanatocin jam’iyar Democract guda 50, da goyon bayan mataimakiyar shugaban kasa Kamala Hariris domin amincewa da kudirin dokar a zauren Majalisar Dattijai da kuma aikewa da kudirin a majalisar wakilai inda jam’iyar Democract ke da rinjaye.
Amincewa da kudirin dokar zai kasencewa daya daga cikin nasarorin da shugaba Biden zai samu a majalisu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Tallafin Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Kangin Talauci
A wani mataki dake zama abun mamaki ga gwamnatin Biden , sanata Joe Manchin ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kudirin na shugaba Biden.
A baya Jihar Virginia ta yamma ta nuna adawa da kudirin, inda ta bayyana tsoron cewa yawan kashe kuɗaɗe zai ƙara yawan tashin farashin kayayaki.
Biden ya tabbatar ma da yan ƙasar ta Amirka cewa idan aka amince da wannan dokar , zata kasence wani babban tarihi kuma zata kasence mai amfani ga kasa baki ɗaya.
Wannan dai na nuni da cewa wani sabon sauyin da aka samu kasencewar sanatocin sun fara amincewa da kudirin.
Haka kuma yana nuna wani sauyi ganin yadda wasu jihohi da a baya suka zaɓi tsohon shugaba kasar Donald Trump ke goyon bayan kudirin.
A wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba shugabanin sanatocin jamiyar Democract , Chuck Schumer da Mr Manchin sun bayyana dalilan su na sauya matsaya inda suka ce 3.5 zia taimakawa kasar Amurka wurin rage yawan fitar da gurɓatance hayaki da kashi 40 nan da 2030.
Sai dai, Mista Manchin da Mista Schumer suma sun ce matakin zai nasar a ta hanyar tara dala biliyan 739 a cikin shekaru goma ta hanyar kara harajin mafi karanci ga manyan kamfanoni zuwa kashi 15 cikin 100, da kara karfafa ayyukan harajin cikin gida da baiwa gwamnati damar yin shawarwari kan takardar sayan maganifarashin magani.
Idan har aka amince da dokar, za ta zama wani gagarumin ci gaba ga shugaban kasar, inda ya tanadi wasu manyan manufofinsa na siyasa, da kuma bayar da damar ceto tsarin tattalin arzikin cikin gida da ya tsaya cik a ‘yan watannin nan sakamakon gazawar tattaunawar.