Ba’a dakatar da Dan majalisa Ayogu Eze ba inji Jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC ta karyata labarin dake yawo a kafafen yada labarai cewa ta kori wani tsohon Dan majalisa Ayogu Eze cewa wannan zancen kangen kurege ne.
Ben Nyowe shugaban Jam’iyyar APC dake Enugu ya bayyana haka ne a wajan wani taron karawa juna ilimi da akayi a Abuja.
KARANTA:-Hukuma masu yaki da ‘yan fasa kwauri na bukatar hadin kan Yan sanda
Ana ruwaito Mr. Nwonkedi Ugwuoke ya rubuta takardar zargin Ayoge Eze da cin amanar jam’iyya sannan ya bayyana dakatar dashi.
Sai dai Jagoran jam’iyyar APC na Jahar ya bayyana cewa a halin yanzu sun Jin dadin jam’iyya da hadin Kai da Kuma cigaban jam’iyya.