Gwamnan Jahar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewar ba’a zaɓe shi Gwamna domin biyan Albashi kaɗai, amma har da samar da romon Dimokuraɗiyya ga Al’ummar Jahar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Mr Mohammed ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin Al’ummar Kiristoci a Jahar, wanda suka kawo mashi ziyarar ban girma sakamakon bikin Kirsimeti a gidan Gwamnati a ranar Asabar.
An ruwaito Gwamnan yana nuna rashin jindaɗin sa, sakamakon chekin kuɗi na Albashi da yawan shi yakai Naira Biliyan 7.
KARANTA WANNAN LABARIN: Muna da burin nan gaba kaɗan mu yi aure — Hassana da Hussaina Ƴan biyun shirin Daɗin Kowa
Yace biyan Albashin Ma’aikata yana hana gudanar da manyan ayyukan cigaba da sauran shirye-shirye.
Gwamnan ya kuma yi masu ƙorafin cewa, wasu Ma’aikatan na karɓar Albashi sau biyu a wata guda,wanda hakan ne ya haifar da Hauhawar yawan kuɗaɗen Albashin.
“Mutane na ƙirƙirar wasu wahalhalu akan yadda ake biyan kuɗaɗen Albashi domin haifar da rashin so a tsakanin mu. Inaga daga cikin mutane dubunnai da muke biya Albashi, dole za’a cire wasu. Gwamnati na biyan kashi 100 na Albashi, kuma zamu tabbatar an cire dukkanin waɗanda basu daga cikin wanda za’a biya Albashi.
Gwamnan yace Gwamnatin sa na bakin ƙoƙari domin tabbatar dacewa Ma’aikatan da aka cire daga jerin waɗanda ake biyan Albashi an maido dasu, musamman da za’a baiwa ƙananan hukumomin cin gashin kansu.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta WikkiTimes ta ruwaito cewar Gwamna Bala Mohammed yana maimaitawa cewa zai gyara yawan Albashin da ake karɓa, Alƙawarin da har yanzu bai cika ba.
Ma’aikata da dama a Jahar, har yanzu suna cigaba da rasa Albashin su, duk da an sanya kwamitoci guda bakwai domin tantance Ma’aikatan bogi, tare da kawo rahoto.
Gwamna Bala Mohammed a lokacin ƙaddamar dashi yace zai cire Ma’aikatan bogi, tare da tabbatar dacewa an biya Ma’aikata haƙƙoƙin su.
Duk da tantancewar da akeyi, har yanzu ba’a samu wani da laifi ba.
Comments 1