Wata Ba’amurkiya mai shekaru 43, mai suna, Jeanine Delsky, ta iso Anguwar Panshekara, wacce ke wajen garin birnin Kano, domin bukatar ta ta auren wani saurayin ta mai shekaru 23, Sulaiman Babayero Isa, wanda kuma sun hadu da shi ne a kafar sadarwa ta yanar gizo.
Ms Delsky, wacce take zaune a California, ta kasar Amurka, ta sauka a filin saukan Jiragen sama na Mallam Aminu Kano International Airport, Kano, ne a ranar Asabar, inda kai tsaye ta shige zuwa anguwar ta Panshekara domin saduwa da iyayen saurayin nata.
Masoyan biyu sun hadu ne a kafar sadarwa ta Instagram kimanin shekara guda da ta gabata, inda suka rika yin musayar hotuna da kuma ci gaba da soyayyar su.
A cikin tattaunawar da ta yi da wakilinmu, Ms Delsky cewa ta yi, ta yanke shawarar biyo saurayin nata zuwa Kano ne a sabili da soyayyar da take yi ma shi.
Ta ce mutane da yawa sun yi sosayya da ita a yanar ta gizo, amma sai ita ta ji ta fi son Isa din ne da gaskiya.
Ba’amurkiyan mai ‘ya’ya biyu ta ce dukkanin su sun yarda da su filfila zuwa kasar ta Amurka, inda suke da nufin su zauna su yi rayuwar su.
Ms Delsky tana rike da hannun masoyin nata tana murmushi, Ms Delsky ta ce ta samu dacewa da abin da take mafarkin so a rayuwar ta.
“Ya aiko mani da sako ta Insgram, inda ya ce mani Hi,” “Amma sai ban karba masa ba, sabili da matsalar da na samu a baya da samarin Nijeriya mayaudara.
“Amma akwai wani saurayin da shi ma yake aiko mani da sako, wanda Sulaiman din ya san shi a matsayin mayaudari, don haka sai ya ce masa ka je ka nemi aikin yi ka daina yaudarar mutanan kirki.” Fadin hakan da ya yi sai na ji kamar shi mutumon kirki ne.”
Sulaiman Isa, wanda ya kare karatun sa na Sakandare ba da jimawa ba, ya ce a shirye yake ya bi budurwar na shi zuwa kasar ta Amurka domin su zauna a can su gina iyalan su.
Ya ce, sam shi bai damu da tazaran shekarun da ta ba shi ba, ya kara da cewa ai hakan ma Sunnan Ma’aikin Allah Annabi Muhammadu (SWA) ne, watau mutum ya auri wacce ta fi shi shekaru.”
Sulaiman Isa, mai sana’ar askin baba, ya nuna fatan da yake da ita na cewa watarana Ms Delsky yana sa ran za ta amshi Addinin Musulunci, ta zama Musulma.
Ms Delsky ta sadu da mahaifiyar Isa, Fatima Sulaiman domin neman amincewar ta.
Mahaifiyar Isa din ta ce ita ba ta da ja a kan soyayyar da dan nata yake yi da Ba’amurkiyan, tana mai yin nuni da cewa za ta ci gaba da yi masu addu’a domin su yi zaman aure a cikin alheri a can kasar ta Amurka. Ana sa ran za a daura auren na su ne a watan Maris.