Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Injiniya Babachir Lawal, ya ki amincewa da Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana zabin Shettima a ranar Lahadi.
Wannan ya haifar da zazzafan cece-kuce a tsakanin jama’a.
Sai dai kuma Babachir, wanda ya kasance mai goyon bayan Tinubu, ya yi Allah wadai da matakin da dan takarar shugaban kasar ya dauka.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da ikonsa a matsayinsa na shugaban kasa kuma mai fada aji a jam’iyyar APC don soke zaben Shettima.
A cewarsa, an isar da ra’ayinsa ga Tinubu da abokansa a kan “matsalolin” na tikitin musulmi da musulmi.
Ya ce a lokuta da dama ya sha yin jayayya a kan cancanta da rashin cancantar samun tikitin biyu a gare shi, sannan kuma a rubuce da baki ya nuna rashin jin dadinsa da irin wannan ci gaba.