• Shugaban Majalissar Dokokin Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani ya bukaci Musulmai da su rungumi sadak.
• Mai taimakami shi kan kafofin yada labarai Ibrahim Dahiru Dan Fulani ne ya bayyana haka acikin wata sanarwa da ya fitar jiya.
• Ya Kuma bukaci al’umar Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci na sallah wurin yiwa Nigeria addu’o’in.
Shugaban shuwagabannin Yan majalissun dokokin yankin Arewacin Kasar nan, Kuma Shugaban majalissar dokokin jihar Kaduna Rt. Honorabul Yusuf Ibrahim Zailani ya bukaci al’umar Musulmai da su rungumi dabi’ar sadaukarwa domin koyi da Annabi Ibrahim amincin Allah shi tabbatar a gare shi.
Shugaban majalissar ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, a cikin wata sanarwa da ya fitar kuma ya bai wa jaridar Dimokuradiyya, ta hannun Mai taimakama shi a kan kafafen yada labarai Ibrahim Dahiru Danfula.
Ya ce” Wannan lokaci ne na sadaukar wa da kuma tausayi kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi yunkurin sadaukar da Dan sa Isma’il, kafin Allah madaukakin sarki ya kawomashi Rago, Kuma ya albarkace da numbin lada” inji shi.
Kazalika hakan ya sa, Zailani ya bukaci Mabiya addinin Musulunci da kadda su gajiya, wurin sadaukarwa da abun da suke dashi ga marasa karfi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano ta dakatar da dukkannin Bukukuwan Babar sallah
Kazalika ya kuma shawarci Musulmai da su fafada irin wanna sadakar, har izuwa ga yan uwa mabiya addinin Christa.
A karshe ya ja hankalin al’umar baki daya da, su yi amfani da wannan lokaci na bikin babbar Sallah wurin yi wa Nigeria addu’o’in samun tabbataccen zaman lafiya mai dorewar, da kuma rokon Allah madaukakin sarki, da ya kawo karshen matsalolin tsaron da ya daddabi kasar na.
Comments 2