Fursunonin ɗari da tamanin da ɗaya a faɗin cibiyoyi uku na gyaran hali a jihar Rivers sun samu afuwa daga babban alkalin jihar, Mai shari’a Simeon Amadi. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Alkalin ya bayyana hakan ne a wajen rufe wani taron kwana biyu a cibiyar gyaran gyaran hali ta Fatakwal a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu Da Haka Jami’an Mu 23 Na Jiran Hukunci A Jihar Kwara—-INEC
Ya ce, wannan wani bangare ne na kokarin rage cunkoso a cibiyoyin gyara hali dake fadin jihar.
Babban alkalin wanda ya samu wakilcin mataimakin babban magatakardar shari’a, Meneme Friday Poronon, yace afuwar na daya daga cikin “bikin shekarar ma’aikatar a jihar ta 2022/2023”.
Ya bayyana cewa fursunonin da aka yi wa afuwar ” an sallamesu kuma an yafe musu ” laifukan da suka aikata.
Babban alkalin kotun Poronon ya kara bayyana cewa, Babban Alkalin jihar ya sake yin wani zagaye a ranar 22 ga Maris 2023 a matsayin wani bangare na ayyukan shagalin shekarar 2022/2023” a jihar.
Ya kuma shawarci fursunonin da aka ‘yantar da su sauya sabon salo rayuwa, ya kara da cewa matakin na daya daga cikin sabbin matakan da aka dauka na “gyara a bangaren shari’a da kuma yadda ake gudanar da shari’ar laifuka a fadin jihar”.
Fursunonin da aka ‘yantar dai su ne wadanda ke fuskantar shari’a kan kananan kararraki da kuma wadanda ke jiran hukunci.
A WANI LABARIN KUMA: El-Rufai Ya Yabawa Soojoji Bisa Hallaka Jagoran Yan ta’adda
Sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda, Dogo Maikasuwa, a wani dajin da ke yankin Gengere-Kaso, daura da kan iyakar Chikun da Kajuru a jihar Kaduna.
Dogo Maikasuwa, an ruwaito shi ne, ya jagoranci wasu munanan hare-hare a kananan hukumomin Chikun da Kajuru na jihar, wadanda ayyukan ta’addanci suka fi shafa a tsawon shekaru