Gwamnatin jihar Neja ta samu tallafin Naira biliyan 1.5 daga babban bankin Najeriya (CBN) domin bunƙasa noman shinkafa da wake da masara da waken suya a jihar.
Tallafin wani ɓangare ne na shirin bunƙasa harkar noma da babban bankin Najeriya na shekarar 2018.
Kwamishinan noman jihar Neja Haruna Dukku ya ce matasa 10,000 ’yan shekara 18 zuwa 35 daga sassan jihar za su ci gajiyar ayyukan noma iri-iri, musamman domin samar a abubuwan more rayuwa a yankunansu.
https://dimokuradiyya.com.ng/kotu-ta-daure-manoma-uku-a-neja-bisa-zargin-yin-fyade/
Kwamishinan ya ƙara da cewa bunƙasa harkar noma na daga cikin manufofin gwamanatin jihar, shi ya sa take ba wa ɓangaren kulawar da ta dace.
Ya ce za a gyara kamfanin casar shinkafa da ke garin Bida wanda ƙasar Koriya ta gina.
Dukku ya ce za a yi gyaran ne bayan ofishin jakadancin ƙasar Koriya ya nuna damuwa game da watsi da aka yi da kamfanin mai shekara 45.
Ya ci gaba da cewa an bayar da aikin ga babban kamfanin sarrafa shinkafa na Elephant Group mai rassa takwas a Najeriya, kuma nan gaba kaɗan za a kammala ƙulla yarjejeniyar.