Bello Turji wanda yayi kaurin suna a Garkuwa da mutane a jihar Zamfara ya ce shi ba mai yin fyade ba ne.
A wata hira da yayi da Mataimakin Editan Jaridar Daily Trust, wanda ake zargin da aikata ta’asa da dama a yankin Arewa maso Yamma, ya musanta zargin da ake yi masa na aikata fyade.
“Mutane na iya fadin abin da suka ga dama. Amma game da fyade, akwai mata a nan. Idan ni mai fyade ne, da na fara da su. Suna son a kai wa Fulani hari ne kawai; ba mu san komai ba akan abun ya shafi fyade.”
“Idan ka dauki lamarin jihar Kano, shin Turji ne ke da alhakin duk laifukan fyade da ake yi a can? Idan kana da hankali za ka san abin da ya wuce matakin Mutum guda”
A kan dalilin da ya sa ya dauki makami, Turji ya ce, “An kashe Fulani ’yan uwana, an kuma sace shanu sama da dubu daya aka kai su Zurmi daga nan aka kai su Maradun. Sarkin Shinkafi yana sane da haka, shi ma sarkin Zurmi ya sani kuma duk jami’an tsaro na lokacin sun san haka. Da na gane ba ni da wanda zan kai kara wajansa, kuma babu wata hukuma da za ta taimake mu, babu yadda za muyi Muna ganin anawa Fulani kisan kiyashi. Ba za mu bari a shafe kabilar Fulani ba a doran kasa. Shi ya sa muma muka dauki makamai.”