Rundunar Ƴan sanda a jahar Zamfara ta samu nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Bello Rugga, tare da kashe wasu ƴan ta’adda guda biyar, a yayin wani samamen da suka kai a ƙaramar hukumar Gummi ta jahar.
Kwamishinan Ƴan Sandan jahar Ayuba Elkanah ya bayyana haka, a lokacin da yake gabatar da ɗan ta’addan tare da wasu mutane 21 da ake zargin ƴan fashi daji ne ga Manema labaru a ranar Asabar a Gusau.
Kwamishinan ya ce “A ranar 1 ga Oktoba na shekarar 2021, Jami’an ƴan sanda da ke yaƙi ƴan ta’adda a kewayen Gummi, sun yi aiki da bayanan sirri inda suka kai hari Gidan Bita, da ke dajin Kagara, tare da cafke wani ƙasurgumin kwamandan ƴan fashin daji, Bello Rugga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bazan taɓa imanin cewa za’ayi Babban zaɓen 2023 a wannan matsalolin tsaro da ake fama a Najeriya — Afenifere
Ƴan sanda sun kama babban Kwamandan Turji, Bello Rugga a Zamfara.
“Wanda aka kama ya kasance babban kwamanda ne ga ƙasurgumin ɗan ta’addan nan ne da ake nema ruwa jallo, wanda aka fi sani da Turji.
“Rugga shine ke kula da yankin Gummi, Gidan Bita, Malanjara da Kagara da ke ƙaramar hukumar Gummi ta jihar.
“Ɗan ta’addan ya kai hare -hare da dama a yankin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da yin garkuwa da wasu da yawa don neman kuɗin fansa,” in ji shi.
Mista Elkannah ya ce wanda aka kama yana tare da ƴan ta’adda da dama a lokacin da aka kama shi, ya ƙara da cewa an kwato bindigogi kirar AK47 daga hannunsa.
A cewarsa, wanda ake zargin a yanzu haka yana hannun ƴan sanda ana gudanar da bincike.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito Kwamishinan ya kuma gabatar da wasu mutane biyu da ake zargi da haɗin gwuiwa, inda ya kara da cewa an kama su ne, a yayin da suke kai miyagun kwayoyi, jakar tabar wiwi da man fetur zuwa sansanin ƴan ta’addan.
Mista Elkanah ya ce wadanda ake zargin sun kuma ambaci wasu abokan hulɗa gami da inda suke sayo kayan maye, yana mai cewa jami’an tsaro na bin diddiƙin wadanda ake zargin.