An tabbatar da mutuwar mutane uku a wani hatsari da ya rutsa da wata babbar mota da kuma babur (Okada) a jihar Legas.
Jaridar PUNCH ta tattaro cewa motar da ba a tantance ba tana dauke da yashi ne a lokacin da hatsarin ya afku a safiyar ranar Talata a kusa da tashar bas ta Eleganza da ke unguwar Lekki a Legas.
Tuni dai aka lalata motar tare da cinna mata wuta, da wasu susatattun munen yankin suka yi.
Hatsarin ya kuma haifar da toshe wasu hanyoyi, inda matafiya da yawa suka tsaya cirko-cirko na tsawon sa’o’i da dama.
Kwamandan Sashen Lekki na Hukumar kiyaye haddura ta kasa, Sani Abdullahi, ya tabbatarwa da jaridar PUNCH faruwar lamarin.
“Tawagar ta da ta je wurin da lamarin ya faru ta tabbatar da cewa mutane uku ne suka mutu a hadarin,” in ji Sani.
Sai dai ya dora alhakin abin da ya haddasa hatsarin a kan gudun wuce kima da direban motar ya yi.