Wani yaro mai shekaru 10 Mai suna Olaniyi Ayomide, ya gamu da ajalinsa a jiya Litinin, ya yin da wata motar da ke kokarin gujewa kamun jami’an tsaro ta afka kanshi.
Lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na daren jiya Litinin, a yankin Ayeyemi na garin Ondo dake karamar hukumar Ondo ta Yamma na jihar Ondo.
Wasu saidun gani da Ido sun shaida wa manema labarai cewa,motar na dauke da alluna ne lokacin da hadarin ya afku.
An ce marigayin yana tafiya a gefen hanya ne, tare da mahaifinsa a kan hanyarsu ta koma wa gida lokacin da lamarin ya faru.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum guda ya mutu, 3 sun jikkata, bayan Sarkin Benin ya haramta aiyukan CDA
Kazalika Wani ganau ya ce, wanda aka kashe da mahaifin nasa ba su da masaniya cewa, direban motar yana kusa da su.
“Direban ya yi kokarin gujewa kamun da Jami’an tsaron Amotekun suka so suyi masa, sannan ya murkushe yaron har lahira,” in ji shi.
Sai dai, Jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC sun dauki gawar marigayin zuwa dakin ajiye gawa, yayin da jami’an Amotekun suka kama direban.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, Nageria na samun rahoton kimanin mutane 15,000 zuwa 20,000 na wadanda maciji ke saran su a kowace shekara.
Karamin Ministan kiwon Lafiya na kasa, Dakta Olorunnimbe Adeleke Mamora, ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin wani taron manema labarai da ma’aikatar ta shirya, don murnar ranar wayar da kan al’uma dangane da illar Sara Macizai ta Duniya.
Da yake tsokaci game da binciken kwana-Kwanan nan Ministan ya ce, mutane 479 majizai ke saran su a Nigeria, cikin mutane 100,000.
Ya kara da cewa, “Najeriya na samun akalla rahoton cizon maciji guda 15,000 zuwa 20,000 a kowace shekara, inda mutane kusan 2,000 suke mutuwa, yayin da mutane 1,700 zuwa 2,000 ake yanke musu kafa ko hannu, don ceton rayuwarsu bayan maciji ya sare su.”
Dakta Mamora ya Kuma bayyana jihohin da aka fi samun rahoton cizon macizai kamar haka: Gombe, Filato, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Benue da kuma jihar Taraba.
Don haka, ya yi kira jihohi, da sauran masu ruwa da tsaki, da su kara zage damtse domin magance matsalar saran macizai.
A nashi bangaren, Babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Mahmud Mamman, ya ce, daga shekarar 2018 zuwa Disamba shekarar 2020, sama da mutane 45,834 macizai suka sare su a fadin kasar nan.
Comments 1