Bappa Mohammed yaya ga gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa manema labarai cewa Mohammed wanda ya kasance Yeriman Duguri ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibitin Turkiyya da ke Turkiyya bayan ya sha fama da rashin lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum Uku Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kaduna
Marigayin ya kasance mataimakin darakta a babban bankin Najeriya kafin ya yi ritaya kimanin shekaru goma da suka gabata.
Ya bar matarsa da ’ya’ya biyar da yayyensa biyu wato; Adamu Mohammed, Wakilin Bauchi da Gwamna Bala Mohammed.
Tuni dai akayi jana’izar marigayin a yau Litinin a kasar Turkiyya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Wani Bene Ya Rufta A Garin Ibadan
Wani gini ya ruguje a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ginin mai hawa uku ya ruguje ne da sanyin safiyar ranar Litinin.