Wata Babbar Kotun Kolin Jihar Kaduna, ta Baiwa Jagoran ‘Yan Shi’a Shaikh Ibrahim Zakzaky, damar tafiya New Delhi na Kasar India, domin Neman Magani.
A lokacin da Kotun ke Karanta Hukuncin Alkalin Kotun ya Ce Lauyoyin Gwamnati sun kasa gamsar da Kotu cewa Akwai Kwararrun likitoci a Najeriya wadanda zasu iya Duba lafiyar Shaikh din a Kasar nan.
Kazalika Kotun ta Ce ta gano bayanan da lauyoyin Gwamnati suka yi a baya na cewa lokacin da likitoci suka zo daga kasar waje domin duba lafiyar Shaikh ba su yi aiki tare da su ba, kotun ta ce wannan ba gaskiya ba ne, inji ta.
Lauyan da ke Kare Gwamnatin jihar Kaduna Barista Dari Bayero, ya Ce zuwa yanzu ba su da ja kan wannan hukuncin amma bai San nan gaba ba, domin zasu je suyi bitar hukuncin kafin su San matsayar su.
Da yake amsa Tambayoyin ‘Yan Jaridu lauyan da ke kare Zakzaky, Barista Falana, cewa yayi dama tuni ya kamata ace Kotu ta barshi ya tafi neman magani domin ana yi ma Wanda yake raye ne Shari’a Ba Gawa ba.
Ya cigaba da cewa Idan suka bari ya rasu a hannun su to wa zasu yi ma Hukunci kenan? Dan haka mun gamsu da wannan hukuncin na Kotu a yanzu.