Wata babbar kotu ta yi hukunci tana goyon bayan mutumin da ya nemi a ba shi damar yawo cikin gari tsirara a cikin titin gari da ke yankin Valencia wanda daga bisani ya je kotun tsirara, Reuters.com ta ruwaito.
KU KARANTA: Mata a Ondo sun fito zanga-zanga tsirara-tsirara saboda rashin tsaro
A wata takarda kotun ta ki amincewa da hukuncin kotun kasa da ita wacce ta bukaci cin tarar mutumin kan yawo tsirara.
Saidai kotun ta ce dokar Spain bata haramta hakan ba. An dauki bidiyon Alejandro Colomar, mai shekaru 29 yana tafe tsirara sanye da takalma kafin aka nemi ya saka kaya kafin ya shiga kotun.
Saidai ya yi jayayya kan yadda aka nemi cin tararsa kan hakkinsa da aka danne. Ya sanar da Reuters cewa ya fara yawo tsirara ne a shekarar 202 bayan yana samun yabo fiye da zagi a al’umma, amma akwai lokacin da wani ya bi shi da wuka.
Spain ta halasta tsiraici tun 1988 kuma babu wanda za a kama don ya yi yawo tsirara kamar yadda dokar ta nuna.
‘Yan Sanda Sun Kame Wasu Maza Shida Bisa Laifin Yi Wa Wata Mata Tsirara
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba, 2022, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wasu matasan al’ummar yankin da yawansu ya haura ashirin suka yi wa matar tsirara tare da yin holinta a ranar 27 ga watan Oktoba, 2022, bisa zargin cewa ta wulakanta wurin ibadarsu ta hanyar tsinke dodon gori a cikinsa.