An sanar da garkame ( babbar Jami’ar dake Bayelsa biyo bayan zanga-zangar da ɗaliban makarantar sukeyi kan karin kudin Makaranta da tsara yanayin shigar Dalibai.
Daliban Makarantar sun gudanar da zanga-zangar lumana a cikin garin Amasoma da Yenegoa babban birnin Jahar, kan karin kudin Makaranta da bada dokar sanya kayan makaranta don daina shigar banza.
Rijistaran makarantar Mista Benjamin Joffa ya sanar da kulle Makarantar.
KARANTA:- Babbar Magana: Ministoci 12 sunyi murabus a India saboda Covid-19
Kamar yadda sakon yazo ” Duba da abubuwan dake faruwa a cikin Makarantar, an bani umarnin sanar da daukacin wadanda ke cikin wannan makarantar an tsaida duk harkoki dake gudana a wannan Makaranta nan take har sai mama ta gani.”
Sannan ana umartar dukkan daliban dake cikin Makarantar dasu tattara inasu-inasu kamin karfe uku.
Shugaban Makarantar Farfesa Ediouminokum ya sanar da rufe biyan kudin makarantar a ranar Litini, inda yace wanda ya biya ya biya wanda bai biya ba za’a korashi gida.
Ya kara da cewa daga yanzu duk dalibin da zai shigo makarantar sai da kayan makaranta, sa’annan Dalibai zasu sayi kayan makarantar ne daga wajan hukumar makaranta.
Tsohon Jagoran IYC yayi kira da’a dakatar da shugaban Makarantar kan dokar da ya saka, yake cewa wannan ai ya keta hakkin Dan adam.
Jagoran ya cigaba da cewa furucinsa na cewa dole kowane dalibi daga ajin kimiyya zai sayi kayan makaranta dubu talatin, sa’annan sauran daliban za su saya akan dubu ashirin wannan ya nuna shi ba uba nagari bane.
Ya cigaba da cewa akwai gidaje da yawa abinci ma wahala yake musu, balantana ace zasu biya wadannan makudan kudaden kan kayan makaranta.
Yace karatu hakkin kowane Dan kasar Bayelsa ne kuma alhakin gwamnati ne da ta bawa kowane mutum dake Jahar karatu Mai kyau Kuma Mai arha.
A lokacin da ake daukan rahotan, Shugaban NDU yana wata ganawa ta musamman tare da Yan majalisun Jahar a Yenegoa.