• An cafke mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Kano
• Wand awake zargin mai suna Aliyu Mohammed Mai shekara 45 ne da haihuwa.
• Dubun ya cika ne a wani Otal, lokacin da yake kan bakin aikin shi na sojan gona.
Jami’an rundunar Yan sandan jihar Kano sun kama wani mutum mai suna Mohammed Aliyu, mai kimanin shekara 45, da zargin yin sojan gona na mukamin Mataimakin Kwamishinan yan sanda wato ACP.
“An sami ingantattun bayanai da ke nuna cewa, Mohammed Aliyu dake zaune a Unguwar Hotoro Mariri na jihar Kano, na a lakanta kanshi da Mukamin ACP” kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a garin Kano.
“Wanda ake zargin yaje wani Otal dake cikin garin Kano, inda ya bukaci aba shi masauki, inda zai sauke wasu bakin shi da sukazo daga Kaduna, da kuma sassan kasar nan, kana ya bukaci a yimishi rangwame, a mastayin shi na Mataimakin Kwamishinan yan sanda” kamar yadda Haruna Kiyawa ya ce.
Haruna Kiyawa ya kara da cewa, Wanda ake zarkin ya bai wa manajar Otal din Katin gayyata mai nauke da sunan shi, a mastayin Mataimakin Kwamishina da Ke aiki a Runduna ta 52 PMF, na garin Chalawa dake Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun sake yin garkuwa da mutun 13 a Kaduna
Aliyu ya sake bayyanawa Manajan Otal din cewa, Shugaban yan’sandan yankin Nassarawa dake jihar Kano Kanin shi ne, Kuma yana aiki ne a karkashin shi.
.
“Kazalika bisa wasu halaye da ya nuna na zargi, hakan yasa Manajan Otal din ya yi hanzarin sanar wa da jami’an yan sanda” inji Kiyawa.
“Kwamishinan yan sandan jihar Kano Sama’ila Shu’aibi-Dikko, ya umarci Shugaban Yan sanda na yankin Nassarawa SP Daniel Itse Amah, da ya isa wurin da lamarin ke faruwa.” a cewars shi.
“Ko da jami’an yan sanda suka Isa wurin, sai suka taras da cewar, Aliyu Mohammed ba Mataimakin Kwamishinan yan sanda ba ne, hakan yasa suka kamashi”, inji Mai magana da yawun rundunar yan sandan na jihar Kano.
Haruna-Kiyawa ya kara da cewa, lokacin da ake gudanar da binciken an sami wasu takaddu da su ke dauke da sunan Ibrahim Muhammad Tijjani, a matsayin Ma’aikacin kiwon lafiya, a hannun Wanda ake zargin .
“A binciken da jami’an yan sanada suka gudanar ya nunar da cewa, Aliyu ba ma’aikacin kiwon lafiya ba ne, kuma ba jami’in dan sanda ba ne”
“Wanda ake zargin ya kuma yi ikirarin cewar, ya yi wasu aikin Tiyata, da kuma bai wa wasu marasa lafiya magunguna” inji jami’in hulda da jama’an.
Bugu da kari ya ce ” CP Shu’aibu Dikko ya bada Umarnin baida laifin ga shashin binciken manyan laifuka ta jihar, domin cigaba da gudanar da bincike.
A karshe Haruna-Kiyawa ya ce, za’a gurfanar da wanda ake zargi gaban Kotu, da zaran an kammala gudanar da bincike.