Yan sandan Moroko dake Lekki sun cafke masu gadi biyu kan laifin satar tiles katan 126, wanda zai kama #447,460. Sannan suka mikasu gaban Kotun majistret don yanke musu hukunci.
Masu gadin sun saci kayan kamfanin Vava wanda Abideen Solanke ke kula da shi. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa
KARANTA:- DA DUMI DUMI: Jiragen yakin da Najeriya ta siyo sun fara isowa
Yan sandan sun ce wadanda ake zargi sune Abbah Dogo mai shekaru 60, da Abubakar Abacha mai shekaru 65 tare da wasu mutane biyu.
Kamar yadda bayani yazo, sun saci kayan cikin dare ne suka sayar dasu, sannan suka tsere.
Sai daga bayan jami’an Yan sanda sukai nasarar cafke su a Lekki dake Legas.
Daya daga cikin su mutumin Borno ne, shine aka mikashi zuwa Kotun Tinibu majistret akan lafin da ake tuhumarsa na sata.
Mike Unah, Jami’in Dan sanda yake sanar da Kotun, ya aikata laifin ne a 20 ga watan June, 2021, a plot 11, Black 12, Admiralty Way, Lekki, Phase 1, Lagos.
Unah ya cigaba da gayawa kotun an dauke shi a kamfanin don tsare kayayyakin dake ciki, amma sai yaci amana ya koma Yana satar kayan ma’aikatan ya gudu, sai daga baya aka samu nasarar cafke shi.