Dr Christian Madubuko, Kwamishinan harkokin kasashen waje, kere kere da fasahar cikin gida, al’adu da yawon bude ido na jihar Anambra ya yi murabus daga mukaminsa.
Takardar ajiye aikin Maduke mai dauke da kwanan wata 11 ga watan Disamba 2020 an raba ta ga manema labarai a ranar Litinin a Akwa.
Tsohon Kwamishinan ya yi zargin cewa akwai “cin hanci da rashawa a gwamnatin jihar” yana mai yin kira ga Gwamna Willie Obiano da ya “tashi tsaye ya zama mai rike da lamurran gwamnatinsa kafin ayi masa kaka gida.”
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Madubuko a shekaru uku da suka gabata ya riƙe muƙamin Kwamishinan masana’antu, kasuwanci da kuma Kwamishinan tituna, layin dogo da zirga zirga.
Wani bangare daga cikin takardar murabus din na cewa: “A kokarin da ake na yaki da cin hanci da rashawa, wasu da ke rike da madafun iko a jihar, sun rika kai suka ta ga gwamnan jihar, domin bata sunana da dora mun laifukan da ban san hawa ba ban san sauka ba.
“ Sun zarge Ni da kawo hargitsi a jam’iyar mu ta APGA, da kuma ba wa gwamnan shawarar tsige Ni kafin na kassara jam’iyyar gaba daya,” a cewar takardar.
Madubuko ya yi ikirarin cewa, a lokuta daban daban, wasu gurbatattun mutane sun sha kawo mashi tayin cin hanci da rashawa amma yana kin karba.