Tsohon gwamnan Jahar Zamfara, Kuma Dan takarar shugabancin Kasa Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, yace zai jaye daga neman kujerar shugabancin Kasar nan ne kawai idan jam’iyyar APC ta baiwa Dan kudu dama.
Yarima dai ya bayyana ra’ayinsa a kan babban zabe dake tunkarowa a 2023 ga manema labarai a Abuja. Kamar yadda Jaridar Thenationnews ta wallafa.
Sanata Yarima cewa yayi banga dalilin nuna bambanci ko kabilanci ba, Koda ace gwamnonin Kudu ba suyi wannan Kiran ba.
KARANTA:- Za mu kama masu sayar da ragunan a kan titi, hukumar FCTA
“Ina mai tabbatar muku, matukar ina raye da yardar Allah ni Ahmad Sani zanyi takarar shugabancin Kasa”
“Amma idan Jam’iyyar APC ta wayi gari tace ta maida dan takarar shugabancin kasa sai dai ya fito daga kudu to zanyi biyayya ga hakan, domin doka ce mai kyau, Kuma kowane Dan jam’iyya zaiyi aiki da ita.”
An tambaye shi ko zai iya barin jam’iyyar APC idan zata cika masa burinsa na baiwa Dan kudu damar tsayawa a matsayin Dan takarar shugaban Kasa., Sai yace a hakikanin gaskiya banda nufin in shiga nan in shiga nan a Jam’iyya.
Daga karshe dai yayi alkawarin ba zai bar jam’iyyar ta APC ba.
“Ni mutum ne mai riko da addini, nayi imani cewar Allah shi ke bada mulki, idan Allah ya kaddara ni zan zama shugaban Kasa to hakan zai faru.”
Ni ban taba sauya jam’iyya ba tun daga farko ina jam’iyyar APP ne muka hade da ANPP sannan muka sake komawa APC, kaga kenan ni Dan asalin APC ne.
Ba nada tunanin sauya wata jam’iyya a siyasa Koda nan gaba.
Idan har akwai maganar Dan takara ya fito daga Kudu to ni na hakura. Sai dai ina da babbacin Allah zai yankeman hukunci akan hakan.