Babban mai horas da ‘yan wasa na Real Madrid, Zinedine Zidane ya kamu da cutar COVID-19. Kungiyar kwallon kafar ce ta sanar da hakan, sai dai ba ta bayar da wasu bayanai kan halin da ya ke ciki ba, ko kuma halin da ‘yan wasan suka tsinci kansu.
KARANTA WANNAN: Kevin De Bruyne Zai Yi Jinyar Makonni Hudu Zuwa Shida
Duk da cewa shan kayi a wasannin da ta buga na kofin, shan kayen da suka sha a hannun Alcoyano ya zo ne bayan mako daya da korarsu daga gasar cin kofin ‘Super Cup’ a hannun Athletic Bilbao.
Ana sa ran dai Madrid za ta kare martabarta na yin wasanni 8 ba tare da shan kaye ba, a yayin da za ta kara da Alaves.
Kungiyar kwallon kafar yanzu su ne a na biyu a kan teburin bayan buga wasanni 18, kusan maki 7 kasa da Atletico, wacce ita ma ke shirin buga wasan ta.