Mutane 2 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata babbar mota ta kutsa cikin shahararriyar cibiyar mabarata da ke kauyen Akinyele a karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo.
Wani ganau ya shaidawa Jaridar City & Crime cewa direban motar ya rasa yadda zai yi ne da Motar, sai ya kutsa kai cikin unguwar inda aka ce an kashe mutane biyu.
Wakilin Jaridar Daily Truat ya samu labarin cewa biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu nan take yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Da take tabbatar da afkuwar lamarin, kwamishiniyar harkokin mata da zamantakewar al’umma ta jihar, Alhaja Kafila Olayiwola ta danganta hatsarin da rashin ingantaccen birki a motar
Ta ce; “Mun samu kiran waya game da hatsarin da ya faru a cibiyar, kuma muka amsa nan take.
“Lokacin da muka isa wurin, wani ganau ya shaida mana cewa wata motar tirela dauke da shinkafa ta ci karo da wata mota a sakamakon gazawar birki, daya ta kutsa kai cikin katangar har zuwa dakin kwanan mata yayin da daya tirelar ta fado kan wani shinge.”
“A halin yanzu da nake magana, wadanda suka jikkata suna karbar magani a wani asibitin gwamnati da ke kusa da inda lamarin ya afku, yayin da aka binne gawarwakin wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.” Inji ta