Daga: Abbas Yakubu Yaura
Yayin da bukukuwan Babbar Sallah ke kara gabatowa, Musulmai masu aminci sun koka kan tsadar ragunan layya a kasuwannin.
Duk da cewa da yawa daga cikin wadanda suka saba yankan dabbobi domin yin layya har yanzu suna da burin sayen naman hadaya, wasu daga cikinsu sun ce rashin karfin tattalin arzikinsu a sakamakon hauhawar farashin kayayyaki na barazanar kawo cikas ga bikin sallar na bana.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zaben-osun-sai-nan-da-shekaru-30-kafin-pdp-ta-iya-kwace-mulkin-najeriya-a-hannun-jamiyar-apc-oyetola/
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar Asabar ne Musulmi a duk fadin duniya zasu gudanar da bukukuwan babbar sallah ko kuma Eid-el-Adha na duk shekara ta hanyar yanka dabbobi domin girmama yadda Annabi Ibrahim ya yi hadaya da abin kaunarsa,Annabi Isma’il, wanda daga baya Allah ya musanya shi da Rago daga gidan aljanna kamar yadda Allah ya umarta. Ana sa ran gudanar da bikin na bana a ranar Asabar 9 ga watan Yuli.
Tumaki, akuya, saniya ko rakumi an yarda a yi hadaya dasu duk da cewa mutane da yawa sun fi son yin amfani da rago saboda lada mai yawa da za’a samu daga wajen Allah.
Wakilanmu masu aiko da rahotannin a fadin jihohin kasar nan sun lura cewa farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi tsakanin kashi 70 zuwa 100 a mafi yawan sassan kasar nan.
Misali, farashin rago mai matsakaicin girma wanda ya kai Naira 30,000 a shekarar 2019 da 2020, yanzu ya koma Naira 50,000, yayin da babban rago na Naira 250,000 ya haura Naira 400,000 a cikin irin wannan lokuta.
Wakilin JARIDAR DIMOKURADIYYA a jihar Kaduna ya rawaito cewa ’yan kasuwa sun karbe manyan kasuwannin dabbobi da kuma wuraren unguwanni don baje kolin raguna iri-iri da girmansu, duk da cewa sun yi ikirarin cewa masu saye kadan ne, saura mako guda kafin zuwan bikin sallar na bana.
A shahararriyar kasuwar dabbobi ta Zango da ke Tudun Wada, cikin birnin Kaduna, daya daga cikin masu sayar da raguna da aka fi sani da Malam Sunusi Usman ya ce dabbobin suna nan amma masu saye ba su zo ba. Ya kara da cewa ana samun farashin dabbobin daya kai tsakanin Naira 50,000 na matsakaita da kuma na Naira 400,000 na manyan raguna.
“Gaskiya idan kana son rago mai kyau na Idi a bana sai ka samu daga Naira 50,000 zuwa Naira 60,000. Wadannan raguna ne matsakaita da masu kyau, amma idan kana bukatar manyan raguna, to kana bukatar daga Naira 100,000 zuwa Naira 400,000,” inji shi.
Sannan yace ya danganta ga tsadar ragunan da sufuri musamman man dizal da ake amfani da shi a motocin da ke jigilar dabbobi zuwa kasuwannin.
A kasuwar raguna ta Kurmin Mashi, Ibrahim Aliyu yace kwastomomi da dama sun yi ziyartan farashin ragunan amma kadan ne suke saya.
Wakilinmu da ya ziyarci kasuwannin raguna guda uku a cikin Maiduguri ya lura da dimbin raguna, amma ‘yan kasuwar sun kasance cikin shakku da fargaba saboda rashin siyar da su. Wuraren sayar da rago daban-daban kuma sun taso a wurare daban-daban a cikin babban birnin jihar.
Wani fitaccen mai sayar da rago a kasuwar Shanu, Babagana Musa, ya koka da rashin samun tallafi sakamakon tashin farashin, inda ya ce, “Rago mai kyau da ake sayar da shi a kan Naira 100,000 a bara yanzu ya kai Naira 170,000. Ana siyar da wani katon rago da ya kai Naira 100,000 zuwa Naira 150,000 a shekarar da ta gabata wanda a wannan lokacin farashin ya canza inda ake samun manyan raguna akan Naira 250,000 zuwa Naira 300,000 a bana. Hakan ya faru ne saboda saurin karuwar abinci.”
A jihar Kano ma haka abun yake yayin da wakilin JARIDAR DIMOKURADIYYA ya kai ziyarar gani da ido kasuwar Darki dake karamar hukumar Wudin duk da cewa an samu saukar ruwan sama a kasuwar amma anyi hada hadar sayar da raguna, inda aka tara Awaki da Raguna.
A zantawar wakilinmu da wani dillalin sayar da raguna Mai suna Ado yace “A gaskiya kasuwar sai godiya akwai kaya babu masaya sosai saboda halin tattalin arziki da muke ciki, inda yace farashin raguna yana kamawane daidai da yadda ragon ko akuya suna kiwatu.
Yace ” ana samun rago na karamin karfi na Naira 30,000, da 40,000 zuwa naira 50,000 inda yace idan kana son kato sai ka saka naira 100,000, 250, 000 harma dana naira 300,000, inda yace abana dai ba sayar da na Naira 400,000 ba.