• Hukumar NSCDC ta baza jami’an ta 1,750 domin tabbatar da tsaro a fadin jihar Kano lokacin bikin babbar sallah.
• Jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
• Hukumar ta bukaci Al’uma su kwantar da hankalin su domin hukumar ta shirya bada tsaro a jihar.
Kwamandan hukumar tsaron al’uma da kare kaddarorin gwamnatin wato NSCDC reshen jihar Kano Mr Abu Abdul Tambuwal, ya amince da baza jami’an hukumar guda dubu daya da dari bakwai da hamsin, domin tabbatar da tsaro a filayen sallar Idi, Masarautu, da sauransu.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar, DSC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar, Kuma ya rabawa kafafen yada labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NIS ta kubutar da Mata hudu a hannun masu safatar mutane
Sanarwar ta bayyana cewa, hukumar NSCDC ta ce, ta dauki wannan matakin ne, domin magance duk wani abu, daka iya kasance wa barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umar jihar, a lokacin bikin Babbar Sallah.
Kazalika sanarwar ta ce, jami’an ta sun shirya Matuka, domin kauda duk wani barazanar tsaro, da ka iya tunkaro wa kafin, lokacin, ko bayan gudanar da bikin sallah.
A karshe ya bukaci Al’uma da su kwantar da hankular su, tun da jami’an hukumar da sauran hukumomin tsaro, na bakin kokarin su, na ganin anyi bikin Babbar Sallah na shekarar 2021 lami lafiya, a daukacin fadin jihar Kano, da ma kasa baki daya.
Comments 2