Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona kuma wanda ya fafata wasanninsa a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Ajax da Liverpool kafin ya koma Barcelona wanda yake ɗan asalin ƙasar Uruguay ne da ake kiransa da suna Luis Suarez ya bayyana cewar da zarar ƙungiyar da ya koma ta Athletico Madrid ta haɗu da Barcelona to babu makawa sai ya zuramusu ƙwallo.
Suarez da Barcelona kusan za a iya cewa ba rabuwar arziki akayiba domin kuwa baran-baran aka rabu rabuwar da ake cewa kora da hali, domin kuwa baki da baki mai horas da Barcelona na yanzu Roland Koeman ya furtawa Suarez cewar bazai tafi da shiba a tawagar sa wato kawai yaje ya nemi sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa.
Bayan ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid ne Leonel Messi ya turamasa da saƙo akan cewar yayi haƙuri da abin da ya faru tsakaninsa da Barcelona inda shima kansa Messi ya nuna jin haushinsa inda yayi kira ga Barcelona akan ta dinga yin rabuwar mutunci da ‘yan wasanta indan an tashi rabuwa bawai irin rabuwar da ba’aso ba azo ana jin hushin juna inda masu iya magana suke cewa anci moriyar ganga anya da kwauranta.
Itadai irin wannan rabuwar tsakanin Barcelona da ‘yan wasa hasali ta ɗakko duba da cewar koda a shekarun baya ‘yan wasa da dama basuji daɗin irin rabuwar da suka yi da Barcelona ba kamar ‘yan wasan Brazil daman mafi yawansu Barcelona bata yin rabuwar mutunci dasu, kamar su Rivaldo da Dani Alves da Ronaldinho da sauransu. Haka irin wannan rabuwar ta faru akan wasu ‘yan wasan Barcelona da basu danganci ƙasar Brazil ba kamar Luis Figo gashi shima kansa Luis Suarez.
Dangane da irin wannan abu sunga izina sosai tunda ga babban misali nan akan Philippe Coutinho bayan sun turashi zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich a matsayin aro inda suka dinga neman kai da shi ga dukkanin ƙungiyar ƙwallon ƙafan da take son sayensa kuma shima har akaji ya furta da bakinsa cewar bayason ya koma Barcelona, sai lokacin da wasa ya haɗa tsakanin Barcelona da ƙungiyar ƙwallon ƙafan da Coutinho yake a matsayin aro a kakar wasan data gabata wato Bayern Munich inda suka ragargaji Barcelona kuma Coutinho shine ya jefa ƙwallo ta 7 data 8.
Hakan ya sanya suka ce sun fasa sayar da shi inda suka dawo da shi tawagar ta Barcelona kuma tuni ya fara bayar da gudun mawa a wasanni guda biyu da Barcelona ta lashe Villarreal daci 4 da nema da kuma wasan da Barcelona ta lallasa Celta Vigo daci 3 da nema wanda duk yadda Barcelona ta kai ga taka leda bata iya lashe Celta Vigo a gida amma wannan karon ta lashe su kuma ana ganin awasan Philippe Coutinho ne ya haddasa dukkanin wata kitimurmurar da akayi nasara.
Shine ake ganin cewar kamata yayi ace hakan ya zamowa Barcelona izina su daina korar ‘yan wasansu tunda kusan duniya ta sani sunyi ƙauran suna ta wannan fanni da rabuwar baran-baran da ‘yan wasansu a duk lokacin da zasu rabu musammman ‘yan wasan da sukayi shuhura.
Idan mun dawo maganar da Luis Suarez ya bayyana game da cewar babu abin da zai hanashi sakawa Barcelona ƙwallo a raga kuwa, ga abin da yake nufi kuma yace:
“Barcelona tsohuwar ƙungiyata ce a halin yanzu tunda na koma Athletico Madrid, mafi yawa idan ɗan wasa ya bar ƙungiya idan suka haɗu har ya sami nasarar jefamusu ƙwallo to sai ya dinga jin kunyarsu baya iya fitowa fili ya nuna murna, to ni gaskiya zamu saɓa akan yadda wasu ‘yan wasan sukeyi, tabbas babu nakawa idan na jefawa Barcelona ƙwallo a raga saina nuna murna ta sosai da sosai kuma zanyi farin ciki da hakan ba tare da tausayin cewar tsohuwar ƙungiyata bace”
Wannan magana da Luis Suarez ya bayyana wasu suna ganin cewar kamar har yanzu akwai haushin korar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta yimasa akan yadda suka rabu kusan ba rabuwar daɗi ba kenan a lokacin da zai koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid.