Babu abinda APC, PDP ke gare su ga Jama’ar Osun — Kwankwaso
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Alhamis yace dukkanin Jam’iyyu biyu na APC da PDP, sun kasa, sai yayi kira ga Al’umma a Jahar Osun da su zaɓi Jam’iyyar NNPP a zaɓen Gwamna na ranar 16 ga watan juli.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikin Kwana 2, Za A Iya Kamo Ƴan Boko Haram Da Suka Tsere — Ali Ndume
A cewar sa, ƙudirin NNPP na karɓe Najeriya ya fara daga Osun, a yayin da dukkanin manyan Jam’iyyu na Ƙasa basu da abinda zasu iya yi. Ya bukaci masoyan sa, dasu zama a shirye a kowane lokaci domin zaɓar Ɗan Takarar Jam’iyyar a lokacin zaben Gwamna.
Kwankwaso, wanda yayi jawabi a Osogbo a taron da NNPP ta shirya, domin gangamin yaƙin neman zaɓe na Ɗan Takarar ta a Osun, Dr Oyelami Saliu, Yayi kira ga masu rajistar Katin Zaɓe da basu karba ba, suje su karɓa, tare marawa Jam’iyyar baya a lokacin zaɓen.
Yace “ƴaƴan Jam’iyyar mu da dama a shirye suke su zaɓi Ɗan Takarar Gwamna na Jam’iyyar mu dake zuwa.
“Magoya bayan mu naso su ga sabuwar Najeriya daga Osun. Tsarin Jam’iyyar mu shine haɗin kai, ba tare da kula ta Ɓangaran ci, Addini a wannan ƙasar. Waɗanda basu karbi Katin Zaɓe suje su karɓa, sannan su zaɓi Jam’iyyar mu.
“Ƙasa zaɓar Jam’iyyar mu domin kawo cigaba mai ma’ana, na nufin baiwa wadancan damar cigaba da mulkar mu. Dukkanin mu, mun san wadannan Jam’iyyun sun kasa mana, kuma babu abinda zasu bada. Mu kore su kawai, kuma wannan ya fara ne daga wannan Jahar.