Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya shawarci gwamnonin kasar nam da su zauna a zaure guda don nemo bakin zaren matsalar da ta addabi kasar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi mai taken “Kasar nan tana Cikin Mawuyacin Hali” Atiku ya ce mafita guda ga matsalar kasar kawai ita ce Gwamnonin kasar su shirya wani gagarumin taro don yi wa tufkar marsalar kasar nan hanci.
Ya ce tantama babu hannu daya ba zai iya daukar jinka ba dole sai an taru, don haka muddin gwamnonin Najeriya su ma a cikin ransu akwai sin kasar, to dole su hada karfi da karfe.
Taohon Mataimakin Shugaban Kasar wanda shine dan takarar shugabancin Kasa na Jam’iyyar PDP a 2019, ya ce batun banbancin jam’iyya shi ma ya kare, muddin kasar aka sa a gaba.
Ya ce matsalar Najeriya ba wai ta kai dan Arewa ne ko wanchan dan Kudu ba, a a sai dai yasu-yasun yan kasar baki daya, don hada kai shine mafita.