Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Dakta Ifeanyi Okowa, a jiya Asabar ya ce yunwa da fatara da ake fama da su a kasar nan na faruwa ne sakamakon rashin tafiyar da tattalin arzikin kasa da jam’iyyar APC mai mulki ta yi.
Ya bayyana hakan ne a wani shiri na karfafawa al’ummar mazabar Ika da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar a majalisar wakilai, Mista Victor Nwokolo, a Boji-Boji Owa, karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Gwamnan wanda ke tare da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar kuma Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a Jihar, Cif Sheriff Oborevwori da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jiha, Cif Kingsley Esiso, sun yaba wa Nwokolo bisa wannan karimcin da ya nuna na bai wa marasa galihu fatan alheri, yana mai bayyana hakan a matsayin “tsarin ƙarfafawa tare da bambanci.”
KARANTA ANAN: Shugaban Yan Bindigar Zamfara ”Bello Turji” Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Ya ce Najeriya ta damu ne saboda mutane na fama da yunwa da rashin aikin yi saboda rashin tafiyar da tattalin arzikin kasa.
Ya kara da cewa hatta dalibai suna fuskantar kalubale da dama saboda iyayensu ba za su iya biya musu bukatunsu ba saboda halin talauci da ya samu sakamakon rashin dacewar gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC.
Don haka Okowa ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa jam’iyyar PDP baya, yana mai cewa ita ce jam’iyya daya tilo da ke da cikakkiyar fahimtar kalubalen da ke addabar al’ummar kasar, kuma tana da cikakkiyar mafita don ceto al’ummar kasar.
A wani labarin kuma: Na Gama Nasara a Zaben 2023 Lokacin Rantsuwa Nake Jira – Dan Takarar Shugaban Kasar PRP
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP, Kola Abiola, ya bayyana cewa zai lashe zaben shekara mai zuwa ta hanyar maimaita irin rawar da mahaifinsa, Marigayi MKO Abiola ya yi a zaben 12 ga watan Yuni, 1993.
Kola ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Abeokuta, ranar Asabar a wajen bikin jana’izar marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, Farfesa David Bamgbose.