By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, Ari Ali, ya ce babu dokar zaman gida a jihar kamar yadda masu fafutukar kafa kasar Biafra suka ayyana.
Ali ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe.
CP na mayar da martani ne ga wani sako da wasu marasa kishin kasa suka wallafa a shafin sada zumunta na Facebook tare da taken “Yan bindigan da ba a san ko su waye ba a jihar Delta na aika sako mai karfi”.
Ya kuma baiwa mazauna jihar tabbacin tsaron lafiyarsu sannan ya bukace su da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal yana mai jaddada cewa rundunar za ta yi taka-tsan-tsan da duk wani ko gungun mutanen da za su yi kokarin haddasa fitina a jihar.
Shugaban ‘yan sandan ya bukaci jama’a musamman mazauna Asaba da daukacin yankin Sanatan Delta ta Arewa da su kasance cikin shiri, su sanya ido tare da kai rahoton duk wani bakon motsi da shakku na jama’a a unguwarsu ga rundunar.
“An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Delta kan wani sako da wasu mutane marasa fuska suka wallafa a Facebook tare da taken “Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a jihar Delta suna aika sako mai karfi”, inda aka gargadi mazauna Asaba da su kiyaye dokar zama a gida kamar yadda aka ayyana ta haramtacciyar kungiyar IPOB.
“Domin a fayyace, Rundunar kwamishinan ‘yan Sandan Delta ta bayyana cewa babu” dokar zama-a-gida” a cikin jihar.
“Ya kamata jama’a, musamman mazauna Asaba da daukacin yankin Delta ta Arewa, su kasance cikin shiri, su sanya ido tare da kai rahoton duk wani bakon motsin mutane a unguwarsu ga rundunar ko wasu jami’an tsaro mafi kusa,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Ali ya ba da cikakken bayani kan jami’an rundunar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana da kuma sanya ido domin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, masu gudan da ayyuka, kwamandojin yankin, DPOs, da kwamandojin dabara da su kula tare da sanya ido a fadin jihar.
Inda ya kara jaddada kira gare su da su yi taka-tsan-tsan da duk wani ko gungun mutanen da za su yi yunkurin haifar da tarzoma, CP ya umurci kwamandojin da su aiwatar da matakan da za su sa Delta ta zama ta gagari ga kowane gungun ‘yan iska.
NAN