Babu Fusatattun Ƴaƴan Jam’iyyar PDP a Katsina – Majigiri
Jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina, ta ce sun hada kai a yunkurinsu na ganin sun lashe zaben 2023 tun daga sama har kasa, kasancewar babu ‘ya’yan jam’iyyar da suke fushi.
Shugaban jam’iyyar PDP na Katsina, Alhaji Yusuf Majigiri, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan wani taro da ƴan takarar jam’iyyar PDP na Katsina a sakatariyar jam’iyyar a kwanakin baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin tsaro: Akeredolu ya caccaki shugaban kasa kan ƙin amincewar AK-47
Taron dai ya kunshi dukkan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a jihar Katsina, wadanda suka tsaya takara kuma suka sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar a 2022.
A cewar Majigiri, matakin hadin kai a PDP ta Katsina, ya nuna cewa jam’iyyar ta shirya tsaf wajen tura sako ga APC, data Shirya fita daga gidan gwamnatin jihar Katsina zuwa 2023.
“A Katsina, ba mu da ‘yan PDP da suka fusata. Ba mu da wani wanda ke zanga-zangar adawa da shugabancin wani ko kuma adawa da takarar wani.
“Wadanda muka sa ran an fusata, su ne wadanda suka fafata a zaben fidda gwani. Kun gansu. Sun hada kai fiye da kowane lokaci kuma suna goyon bayan takarar wadanda suka fito.
“Mun gama ganawa da su duka. Suna nan a hedikwatar PDP ta Katsina domin nuna goyon bayansu ga dukkan ’yan takara a kowane mataki.
“Ku tuna, na tsaya takarar gwamnan jihar tare da Sanata Yakubu Lado, Architect Ahmed Aminu, da Shehu Inuwa Imam. Muna nan duka. Babu ɗayanmu da ya koma wani jam’iyya. Haka kuma ‘yan takarar majalisar dattawa da na wakilai.
“Abin da muke bukata mu samu nasara a jihar shi ne hadin kai. Musamman bangaren wadanda suka yi sha’awar shiga ofisoshi daban-daban da kuma masu neman mukami sun hadu a kowane mataki.
“Muna kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihohin da ke fama da rikici da su yi koyi da PDP ta Katsina ta hanyar hada kai yayin da ake fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya nan da ranar 28 ga watan Satumba,” in ji Majigiri, Shugaban PDP na Katsina.
Tun da farko kafin karbar ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Majigiri ya ce, jami’an jam’iyyar sun kuma ganawa da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar PDP a jihar ciki har da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 34, inda suka tattauna tare da tsara taswirar kwamitin yakin neman zaben ta tun daga rumfunan zabe har zuwa mazabun kananan hukumomi da matakin jiha.
A wani labarin kuma: Yobe ta Arewa: Machina ya yi wani jawabi kan hukuncin Kotu
Dan takarar kujerar Sanatan jihar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Bashir Sheriff Machina, ya yaba da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke masa a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC na gaskiya inda ya bayyana hakan a matsayin nasara na adalci.
Machina, wanda ya mayar da martani kan lamarin ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Husaini Mohammed Isa a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya kuma yi kira ga daukacin magoya bayansa da al’ummar Yobe ta Arewa da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda.