Babu Kokwanto Tinubu Zai Lashe Ƙuri’un Jahar Kaduna a 2023 — Sanata Uba Sani
Sanata Uba Sani wanda shine Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar APC ya ce ko tantama ba shi da shi cewa ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC ne zai lashe jihar Kaduna a Zaɓen Shugaban Ƙasa da za a yi a 2023.
Sanata Uba Sani ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi akan Ƙaddamar da Shettima a Matsayin Abokin Takarar Tinubu a Zaɓen 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NPC Ta Yunkuro Gabanin Aikin Kidayar 2023
” Ina so ku ɗauki takarda ku rubuta, ku ce nine na faɗi, a Jihar Kaduna Tinubu da Kashim Shettima ne za su kwankwaɗi madarar ƙuri’un mutanen Kaduna. Kuma ina tabbatar muku cewa za ku faɗi na ce haka bayan zaɓe ina so ku shaida haka” Inji Uba Sani.
Uba ya ƙara da cewa mutane na yi wa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shiga sharo ba shanu, su na yanke hukunci a kansa akan abubuwan da basu sani ba, bayan kuma ba haka bane.
” Ina son in gaya wa duniya cewa shugaban mu kuma Gwamnan mu mai adalci, Nasir El-Rufai ne ya fara kiran Kashim Shettima bayan Tinubu ya bayyana shi a matsayin Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC.
“Amma kuma maliya da masu hassada suka garzaya wasu kafafen yaɗa labarai suka riƙa kantara masa ƙarya, suna faɗin wani abu daba haka ba.
” El-Rufai na tare da wannan zabi sannan yana tare da Tinubu 100 bisa 100.
Bayan haka sai Sanata Uba Sani ya ƙaddamar da Kashim Shettima shugaban kungiyar Matan Arewa masoya Tinubu wanda a wurin wannan taro ya kwarzanta Shettima da Tinubu da yi musu alƙawarin lallai za su yi aiki tukuru wajen ganin su ne suka yi nasara a jihar Kaduna idan zabe ya zo.