Tun bayan rantsar da gwamnatin Apc a matakin jiha, Anan katsina aka fara wata Shari’a wadda tak’i ta k’are, inda gwamnatin jiha k’ark’ashin Mulkin Aminu bello Masari, take zargin tsohon gwamnan da kwashe Wasu kudi babu gaira babu Dalili.
Wanda mu a wurinmu ta zama kamar wasan Kwaikwayo mai dogon zango, Wanda ake kashe lokaci Mai yawa ba’a k’arasaba.
Dukda dama Wasu sunyi zaton faruwar hakan duba da cewa Wanda ake k’ara kwararren lauyane.
Inaganin kawai asarar kudi data lokacine akeyi, tunda Haryanzu angaza cimma matsaya, maana angaza yanke hukunci Mai gaskiya ya kwashe gaskiyarsa.
Inaganin da gwamnatin Aminu Bello Masari zata duba tsawan shekarunnnan da aka kwashe angaza lalubo al’k’ibla Tama ta janye k’arar zaifi adawo kawai a fuskanci gaba.
Domin na lura kusan du jihohin arewa babu irin wannan Shari’ar sai anan katsina, kuma Haryanzu babu Wanda keda yak’inin nasara, Don kowa cewa yake shine mai nasara tsakanin jam’iyar PDP da Apc.
Maigirma gwamna ya kamata kawai a share abinda ya wuce a fuskanci gaba, Don talaka ya amfana.