Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya ‘National Economic Council’ (NEC) ta karyata batun cewa gwamnatin tarayya buga takardar kudi domin inganta kason jihohi a watan Maris.
Sannan, NEC din ta kuma yin fatali da ikirarin gwamnan babban bankin Nijeriya da ke cewa bankin na da damar yin hakan.
Tun da farko ma dai gwamnatin ta shure batun da gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya yi na cewa an buga takardar kudi na biliyan 50 zuwa 60 domin raba wa jihohi.
Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewar gwamnati ba ta buga kudi domin ta watsar a kan titi ba, illa dai don ta baiwa gwamnati.
A sanarwar da NEC ta fitar a yau din nan karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta hakikan ce kan cewa babu wani kudin da gwamnati ta buga.