Hukumar yiwa ƙasa hidima ta (NYSC) ta ce ba za ta bude sansanoninta ba har sai yanayin annobar COVID-19 ta yi sauki a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta sanar da hakan cikin wata takarda da ke karyata jita-jitar cewa za ta bude sansanoninta a fadin Najeriya.
Takardar da Darakktan Hulda da Jama’ar NYSC Adenike Adeyemi ya fitar, ta jaddada muhimmancin lafiyar masu yiwa ƙasa hidima da ma’aikatanta da sauran mutanen da ke alaka da sansanonin ga ga hukumar.
“Wannan na daga cikin dalilanmu na rufe rukunin (Batch A) na matasa masu yi wa kasa hidima a watan Maris, 2020. Ba za mu taba yin abin da zai kawo barazana ga lafiyarsu ba.”
Hukumar ta ce ko da ta tabbatar cewa annobar ta lafa, ba za ta bude sansanonin ba har sai Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude sansanonin.
Ta kuma yi kira ga matasan da wadanda suke bisa layin fara shirin da su yi watsi da duk wani labari da za su ji kan sansanonin matukar ba daga hukumar labarin ya fito ba.
Ta ƙara da cewa shugaban hukumar Shuaibu Ibrahim, na kiran matasan da su ci gaba da kiyaye ka’idojin kariya daga kamuwa da annobar, kamar yin amfani da kyallen rufe fuska da wanke hannu da dai sauransu.
Inda ya tabbatar da cewa lafiyarsu ita ce gaba da komai.