Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya ce babu ranar janye dokar hana fitar da ya kafa a daukacin jihar don dakile yaduwar annobar Korona.
El-Rufa’i ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake ganawa da wasu kafafen yada labarai dake jihar ta Kaduna a ranar Talata, inda ya ce ba shakka akwai shiri a kasa na sassautawa da ma janye dokar hana jama’a fita baki daya, amma gwamnati ba ta soma nazari kan ranar aiwatar da matakin ba.
Nasir El-Rufa’i ya ce kafin tunanin tsayar da ranar sassautawa ko janye dokar hana fita a Kaduna, tilas sai wadansu ka’idoji sun cika, da suka hada da kara yawan mutanen da jami’an lafiya ke yiwa gwajin cutar a jihar, da kuma tabbatar da cewa an tabbatar da aikin dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin Nijeriya.