Babu shakka babban taron jam’iyar APC zai gudana ne a mako mai zuwa—- Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce bagudu baja da baya ka ranar da za’a gudanar da babban taron jam’iyyar APC Mai Mulki.
Gwamnan wanda ya yi magana da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja ranar Talata, ya ce an fara shirye-shiryen gudanar da babban taron.
Ganduje wanda shi ne Shugaban kwamitin kula da wasu kananan Kwamiti na taron ya ce an fara horas da jami’an da zasu kula da gudanar da zaben.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa an ga matasa maza da mata wadanda ke cikin kwamitin a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, domin horas da su gabanin babban taron.
Ganduje ya ce, “Muna shirye-shiryen gudanar da babban taron. Baya ga zaɓen ƙwararrun matasa maza da mata kimanin 250, ana ci gaba da atisaye bayan an kammala za su wuce dandalin Eagle Square wurin da za a gudanar da babban taron.
“Zan kasance a wurin da kaina tare da sauran membobin kwamitin tsare-tsare. Ka san za a samu manyan mutane da yawa; ‘yan majalisa, gwamnoni, shugaban kasa da mataimakinsa, har ma ministocin da za su kasance a wurin a matsayin masu sa ido, ko Kuma Wani fannin.
Dangane da umarnin kotu na dakatar da taron, Ganduje ya ce, “Ba ni da shakku. Taron mu zai gudana insha Allahu. Kada ku damu mun shirya ma Taron.