Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa ba ta da sha’awar tattaunawa da ‘yan bindiga domin yi sulhu, saboda sun yi watsi da damar da aka basu tun da farko.
Gwamnan ya bayyana hakanne a garin Gusau Babban Birnin jihar, inda yake cewa, a maimakon haka, jami’an tsaro za su fatattaki Yan bindigan a fadin jihar baki daya.
A yayin da yake jawabi ga jama’a Matawalle ya ce, “Gwamnatina ba za ta sake yin afuwa ga yan bindiga ba, saboda sun kasa rungumar shirin zaman lafiya da aka fara yi musu tun da fari.”
KARANTA WANNAN LABARIN: NNPC Bai Samar da ko si-si ba, ya biya ma’aikata albashin Billiyan 60
Gwamnan ya ce, yawan hare -haren da jami’an tsaro ke kaiwa Yan tada kayar baya a jihar, ya tilastawa Yan bindigan fara Neman gwamnati donmin neman tattaunawa.
Kazalika Gwamna Matawalle ya gargadi yan siyasa da su guji bai wa yan ta’adda, ko wani irin tallafi.
Gwamnan ya ce gwamnatin Zamfara za ta gurfanar da duk wani dan siyasa da aka kama da hannu, a cikin aiyukan ta’addanci a jihar.
A karshe Gwamna Bello Matawalle ya Kuma bukaci mazauna jihar baki daya, da su kasance masu hakuri da goyan bayan, kan sabbin matakan tsaro da aka sanya, don fatattakar yan ta’adda da abokan aikin su a jihar Zamfara, don dawo da dauwa-mammen zaman lafiya a fadin jihar.