Mai horas da Yan Wasan kasar Spaniya Luis Enrique ya fitar da jerin sunayen yan wasansa da za su fatata gasar EURO ta shekarar 2020 ba tare da sunan Kyaftin din Real Madrid Sergio Ramos ba.
To sai dai Enrique ya kira dan wasan Manchester City Aymeric Laporte wanda bai jima da sauya kasa ba.
Ramos mai shekara 35 ya yi ta fama da matsanancin raunuka a wannan inda ala tilas sau biyar kachal ya fafata wasa a wannan shekara.
“Wannan mataki ne mai tsarkakiya, to amma kowa ya san bai samu damar fafaa wasanni ba kamar yadda ya kamata, kuma ya sha wahala matuka wajen atisaye” Cewar Enrique.
Rashin sanya sunan Ramos din na nuni da cewa kenan yanzu haka babu dan wasan Real Madrid ko da guda ne a jerin yan wasan na Spaniya.
Shi dai Laporte mai shekara 26 an haife shi ne a Kasar Faransa, kuma tawagar kasar ta kira shi gar sau uku, to amma bai samu damar fafata wasa ko da guda ba wa kassr.
Da ma kuma Enrique na fuskantar karancin yan wasan baya tunda dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ya yi ritaya wa kasar ta Spaniya a shekara ta 2018.