Gwamnatin jihar Yobe sun nemi da ‘yan Nijeriya su yi watsi da rahoton da yake cewa an samu wanda ya mutu sakamakon cutar Korona a jihar.
Jaridar Daily Trust ta labarto cewa Alhaji Muazu Brahji Darakta a ma’aikatar lafiya ta jihar ya rasu a cibiyar killace al’umma na asibitin jihar dake Damaturu a ranar Laraba.
Dan uwan mamacin Yau Ubaliyo Abubakar, ya shaidawa majiyarmu cewa dan uwan nasa a ranar Laraba aka dauke shi aka kais hi asibiti, inda ya rasu a ranar Laraba, sai dai ya ce an yi masa gwajin cutar Korona wanda har yanzu suna jiran sakamakonsa ne.
Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da ba su da cibiyar gwajin cutar Korona, inda mafi yawan wadanda ake yiwa gwajin cutar ana kai wa ne Abuja ne ko Borno domin tantance sakamakon gwajin.
Mamman Mohammed, wanda shi ne Daraktan hulda da kafafen watsa labarai ga gwamnan Yobe a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis ya karyata batun cewa wani a jihar ya mutu sakamakon cutar, inda ya ce jihar Yobe ita ce jiha ta farko a Nijeriya da bisa rajin kanta ta nemi a gwada wani, kuma karshe sakamakon ya nuna ba shi da.